Jinjiri Giwa Mai Ƙwanƙwanto
Judith Baker
Wiehan de Jager

Kowa ya san da giwa tana da babban hanci.

1

Amma can dauri, hancin giwa babba ne kuma yana da girma. Hanci ya yi kamar takalmi saman fiskarta.

2

Wata rana sai giwa ta aifi wani jinjiri mai ƙwanƙwanto. Jinjiri giwar tana da yawan tamabayoyi ka kowace dabba.

3

Yana mamakin raƙumin daji. "Don mi kake da dogon wuya" in ji jinjirin giwar.

4

Yana mamakin karkandam. "Don mi ƙafonka yake da tsini?"

5

Yana mamakin dorina. "Don mi kike da jan ido?" jinjirin giwar yake tambaya.

6

Kuma yana mamakin kado. "Mine ne abincika na dare?"

7

"Kar ka ƙara faɗin haka!" in ji ma'aifiyarshi giwa. Sai jinjirin ya yi nisa da ita yana susar ido.

8

Amma da yake hankaka yana da wayo sai ya ce mishi: "Ka biyo ni bakin tabki. A nan kana ganin abin da kado yake ci da dare."

9

Jinjiri giwar ya bi bayan hankaka har bakin tabki.

10

Ya ratsa ciyawa kuma ya tsaya bakin tabkin. Ya dubi ruwan. Ina kadon yake?

11

"Ina kwana", in ji wani dutsi a bakin ruwan. "Lafiya lau", in ji jinjirin giwar. "Ko zuku iya gaya mini abun da kada yake ci da dare?"

12

"Duƙo in kaya maka" in ji dutsin. "Matso, matso ka ji" Jinjirin giwar ya duƙo, har.

13

"Wup!" hanci cikin bakin kado. "Kado, mi kake ci da dare." Hankaka yake faɗi.

14

Jinjirin giwa ya ja, ya ja tun ƙarfinshi ya kasa. Amma kado ya ƙi ya saki.

15

Jinjirin giwa, ya ja, ya ja, ya ja har "Dum!" ya faɗi bisan bayanshi.

16

Kado ya ji haushin abincinshi ya kubce mishi.

17

Jinjirin giwa ya dubi hancinshi. Bai ga ƙarshen hancin ba.

18

Hancin ya yi tsawo, kamar ya miƙa shi saman icce ya ciro wani abu.

19

Ya iya kuma ya shaƙo ruwa masu zafi.

20

Tun daga shi ne, giwa take da dogon hannu, kuma take amfani da shi.

21
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Jinjiri Giwa Mai Ƙwanƙwanto
Author - Judith Baker, Lorato Trok
Translation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid
Illustration - Wiehan de Jager
Language - Hausa (Niger)
Level - First sentences