Mi Ƙanwar Idi?
Nina Orange
Wiehan de Jager

Wata rana da farar safiya, kakar Idi ta yi kiran shi, "Idi, don Allah, kana iya kai ma ma'aifanka wannan ƙwan? Suna son su yi wani babban biskiti na auren ƙanwarka."

1

Lokacin da yake zuwa gida ma'aifan nashi, Idi ya gamu da wasu samari biyu suna cirar ƴaƴan itace. Ɗaya daga cikin yaran ya ɗauki ƙwai ɗaya kuma ya jefa saman iccen. Ƙwai ya fashe.

2

"Mi ka yi?" in ji Idi. "Wannan ƙwan na yin biskiti ne, biskitin auren ƙanwata. Mi ƙanwar tawa za ta ce idan babu biskitin auren ta?"

3

Samari ba su ji daɗin wannan wasan da suka yi ma Idi. "Babu yadda za mi yi don yin biskiti, amma ga wannan sandar ka kai ma ƙanwarka." In iji ɗaya daga cikin su. Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.

4

Bisan hanya, ya tarda mutane biyu suna gina wani gida. "Muna iya amfani da wannan sandar taka mai ƙwari?" in ji ɗaya daga cikin mutanen biyu. Amma da yake sandar ba ta da ƙwari sosai, sai ta kariye.

5

"Mi kuka yi?" in ji Idi. "Wannan sandar kyauta ce aka ma ƙanwata. Masu ciran ɗiyan itace suka ba ni don sun fasa ƙwan da za yi biskitin auren ƙanwata. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu ba ƙwan, ba biskitin kuma babu kyauta ko ɗaya." Mi ƙanwar tawa za ta ce.

6

Maginan ba su ji daɗi ba da suka karya sandar. "Ba mu san abin za mu yi ba, amma ga ciyawa kaɗan ka kai ma ƙanwarka," in ji ɗaya daga cikinsu. Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.

7

Bisan hanya, Idi ya tarda wani makiyayi da saniya. "Wannan ciyawar sai ta yi daɗi, ko ka ba ni kaɗan?" in ji saniyar. Sai da yake ciyawar tana daɗi, saniyar ta cinye duka.

8

"Mi kika yi?" in ji Idi. "Wannan ciyawar, kyauta ce aka ma ƙanwata. Magina sun ba ni ciyawar don su karya sandar cirar ɗiyan itace. Masu cirar ɗiyan itace sun ba ni sandar don sun fasa ƙwan yin biskitin auren ƙanwar tawa. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu babu biskitin, ba kuma kyauta ɗaya. Mi ƙanwar tawa za tace?"

9

Saniya ba ta ji daɗi ba da ta cinye ciyawar. Makiyayin ya ɗauki niyyar bada saniya don tar aka di kuma ta zama kyauta ga ƙwanwarshi. Idi ya ci gaba bisan hanyarashi.

10

Sai dai lokacin da za a yanka saniyar, sai ta gudu ta koma ga mai ita. Idi kuma ya ɓadda sawunta. Ko da ya zo wajen auren ƙanwar tashi, mutane sun yi abincin.

11

"Mi za ni yi?" in ji Idi. "Saniyar da ta gudu, kyauta ce kambacin ciyawar da magina suka ba ni. Magina sun ba ni ciyawar don sun karya sandar cirar ɗiyan itace. Masu cirar ɗiyan itace sun ba ni sandar don sun fasa ƙwan yin biskitin auren ƙanwar tawa. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu babu saniyar, ba biskitin, ba kuma kyauta ɗaya."

12

Ƙanwar ta Idi ta yi tunani kuma ta ce: "Idi ƙanena, ban damu da wannan kyautar. Ban damu da biskitin ba. Yau ranar murna ce, ina farin ciki. Sanya tufafinka na salla ka zo mu raya wannan ranar!" Sai idi ya yi hakan.

13
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Mi Ƙanwar Idi?
Author - Nina Orange
Translation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid
Illustration - Wiehan de Jager
Language - Hausa (Niger)
Level - Longer paragraphs