Farkon Zuwana Kasuwa
Timothy Kabare
Catherine Groenewald

Ni mazamnin garin Kakuma ne, wurin hamada ce, akwai zafi ƙwarai, da itatuwa masu ƙaya, awakin garin sun fi mutanen yawa. Kasuwa garin ma shiru ne, sai ƴan rumfuna. Ma fi yawan mutanen saman keke suke tafiya.

1

Wata rana, ma'aifiya ta kiranyo ni ta ce mini, "Sani, yau ka cika shekaru shidda. Za mu ba ka wani albishir." "Mine? Mine?" na matsu in sani. "Gobe, za mu tafi kasuwar A-ci-da-kofato cikin mota," in ji ita, "Za mu tafi tare da kai!" Farko tafiyata maraya! Na kwana ina jin daɗi, ban yi barci ba don murna.

2

Washe-gari, a tashar Kakuma, na riƙe wannun mamata da na tantita ina sanye da sabbin kaya. Ga ni nan ɗan ƙarami tsakanin mamata doguwa ramamman da tantita mai jiki.

3

Motar ta cika kuma ni ina zamne saman gwiwar mamata. Zafi da gajiya kuma da murna sun sanya na yi barci tsawon bulaguron kuma ban yi kallo ba.

4

Rana ta yi sosai ko da muka iso kasuwar A-ci-da-ƙofato. A bakin kasuwar akwai wata mata tana saida hatsi. Gaban kaɗan, wani mutum yana shirin fara saida dankali. Cikin wani lungu, akwai wata ƙaramar mata, da take ɗauke da wani jirgi na roba bula da yake ta haskawa. Jirgin na wasan yara ne. "Maman, maman, dubi wannan jirgin." Amma ta ja ni ta hannu, muka tafi gaba.

5

A tsakiyar kasuwar, akwai wata babbar rumfa da ɗiyan itace iri-iri. Wasu na san su wasu ko ban taɓa ganinsu ba. "Mi sunan wa'ƴanda ɗiyan itacen?" na tamabayi mamata. Tana gwada mini kuma tana faɗa mini: "Lemun zaƙi ne da gwaiba." Na juya na ce, "Wa'ƴannan fa?"

6

Duk cikin ƴaƴan itacen, na fi son tuffa. Ina son shi ƙwarai. Ina son in ji ɗanɗanonshi. Sai na ce ma mamata: "Kina iya saya mini guda?"

7

Ko da ta miƙo mini tuffar sai na sanya hannu biyu na karɓa, kuma na fara kurkurar wurin daɗin. Ban taɓa jin daɗin ɗan icce kamar wannan. Shi kaɗai nake so.

8

Bayan na gama cin tuffar, sai na ɗaga kai sama don in ma mamata magana. Amma ban gan ta ba. Sai na dubi ta hanyar da muka zo, kuma ban gan ta ban ga ba tantita. Na duba dama da hagun amma ban gan su ba. "Ba ku ga mamata?" nake tamabayar mata masu saida dankalin turawa. Ba su ce mini komi ba. Sai na fara kuka.

9

Bayan ɗan lokaci, wata mata ta kama hannuna ta kuma kai ni wani wuri da ke akwai yara. Wani mutum mai gemu da yawa ya tamabaye ni, "Mi sunanka yarona?" "Sa-ni," na ce mishi cikin kuka.

10

Ina tambayar kaina, in yaran sun zo kasuwa ne suma. Sai na bar kuka don in ga ba wani yake cikin ɗaki yana sayan yaran. Sai ga wata mata ta zo ta tafi da wani yaro. "Ni zan bi bayan shi," nake tunani. "Kenan ba ni ba komawa gida," Sai na fara kuka kuma.

11

Lokacin da na ji mutum mai gemu ya ce: "Ina Sani?" sai na ci gaba da kuka ƙwarai. "Ban tafiya tare da ku!" ina kuka. Sai na ruga na kuje mishi.

12

Ko da mamata da tantita suka ji an kama sunana, sai suka rugo cikin ɗakin "Sani, Sani," ake kira da wata murya sananniya. Mamata ce.

13

Lokacin na zabura in rungumi uwata sai tanti ta ce, "Sani mun ta neman ka don mu ba ka wata kyauta don ganin cikon shekarunka shidda." Sai ta fiddo daga cikin jikarta wannan jirgin na roba na gani. "Naka ne," ta ce.

14
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Farkon Zuwana Kasuwa
Author - Timothy Kabare, Ursula Nafula
Translation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid
Illustration - Catherine Groenewald
Language - Hausa (Niger)
Level - Longer paragraphs