Ayabar Kaka
Ursula Nafula
Catherine Groenewald

Garkar kaka tana ban shawa, akwai dawa, da hatsi kuma da rogo. Amma ma fi mahimmanci shine ayyaba. Koda yake kaka tana da jikoki da yawa, na sani da ni ta fi ƙwauna. Tana gayyata ta a gidanta. Tana gaya mini abubuwa da dama. Amma akwai abin ba ta gaya mini: Wurin da take nana ayaba.

1

Wata rana, na ga wani babban kwando na haki ajiye cikin rana a gaban gidan kaka. Da na tambaye ta, mine ne amfanin Kwandon, sai ta ba ni amsa kamar haka: "Kwandon mamaki ne." A kusan kwandon, akwai ganyen ayaba da kaka take jujjuyawa lokaci suwa lokaci. Na yi mamaki. "Mine ne amfanin wannan ganyen kaka?" na tambaye ta. Sai ta ba ni amsa kamar haka: "Ganyen mamaki ne."

2

Akwai shawa in kana kallon kaka, ayaba, ganyen ayaba da kuma babban kwandon na haki. Amma kaka ta sanya ni in kiranyo ma'aifiyata don nemo wani abu. "Kaka, don Allah, bar ni in ga abin da kike gyarawa" "Kar ki zama maras ji, jikata, ki yi abin aka ce ki yi" kaka take faɗi. Sai ni kuma in tafi da gudu.

3

Bayan na komo, kaka tana zamne waje, amma ba kwando, ba ayaba. "Kaka, ina kwando, ina dukkan ayabar, kuma ina" Sai ta ba ni amsa kamar haka: "Suna wani wuri na mamaki." Ban ji daɗi ba.

4

Bayan kwana biyu, kaka ta aike ni cikin ɗakinta in ɗauko wata sanda da take tokarawa ta yi tafiya. Ko da buɗe ƙofar sai ƙamshi nunannan ayaba ta tarbo ni. Tsakar ɗakin, akwai babban Kwandon mamaki na kaka. An ɓoye shi cikin wani babban bargo. Na ɗaka shi na ji wannan ƙamshi mai daɗi.

5

Sai na ji muryar kaka, na zabura, "Mi kike yi? Ki yi maza ki kawo mini sandar." Ni kuma na yi maza na ɗauko sandar. "Mi kike ma murmushi?" in ji kaka. Tambayar tata, ta sanya na gano da cewa, murmushina na gano wuri mamakin da kaka take faɗi.

6

Washe–gari, lokacin da kaka ta zo ta ga ma'aifiyata, ni kuma sai na ruga gidanta don in ƙara ganin ayabar. Akwai da yawa da suka nuna. Na ɗauki ɗaya na ɓoye cikin rigata. Bayan na gano kwando, sai na laɓe bayan ɗaki na canye da sauri. Ban taɓa cin ayaba mai daɗin wannan ayabar.

7

Washe–gari, lokacin da kaka take cikin garkar tana tattara gayan garka, na sake komawa cikin ɗakin nata don in ga ayabar. Sun fara nuna. Ban yi haƙuri ba kuma na ɗauko hudu. Ina fitowa sannu sannu sai na ji kaka ta yi wani ɗan tari waje. Na ɓoye ayabar cikin riga, kaka kuma ya wuce.

8

Washe-gari, ranar kasuwa ce. Kaka ta tashi tun da safe. Kullum tana kai ayaba da rogo don ta saida a kasuwa. Ranan nan, ban je ba na gaida kaka. Amma zan je in iske ta.

9

Can da maraice, babana da kaka sun kiranyo ni. Ni san abin da na yi. Daren nan, da na kwanta, na yi tunanin da ba ni ƙara satar kakata ko ma'aifina ko wani can daban.

10
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Ayabar Kaka
Author - Ursula Nafula
Translation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid
Illustration - Catherine Groenewald
Language - Hausa (Niger)
Level - Longer paragraphs