Babbar shuɗiyar mota
Mecelin Kakoro
Mango Tree

Babbar mota ɗaya ce tak a ƙauyen su Tanko. Babba ce, kuma shuɗiya. Tana da ƙara sosai.

1

Gobe za mu je gari, inji mahaifiyar Tanko. "Za mu sayo kayan makarantarka."

2

Tanko ya yi murna sosai. Za su yi tafiya a babbar shuɗiyar mota. Bai yi barci ba wannan daren.

3

Yayin da mahaifiyarsa ta je tada shi, Tanko ya rigya ya shirya.

4

Tanko da mahaifiyarsa sun je inda motar ke tsayawa. Sun jira babbar shuɗiyar mota, amma motar ba ta zo ba.

5

Wasu mutane sun isa wurin tsayawar mota. Suna ƙorafi saboda motar ta makara. "Ina motar?" Suka tambaya.

6

Tanko ya damu. "Ba mu da damar zuwa gari," ya yi tunani. Ba zai samu kayan makaranta ba.

7

Wasu mutane suka haƙura, suka koma gida. Tanko ya yi kuka, bai son ya koma gida. "Za mu jira kaɗan," in ji mahaifiyarsa.

8

Nan take sai suka ji ƙara. Suka ga ƙura na tashi a sama. Motar tana zuwa!

9

Amma motar ba shuɗiya ba ce, ba ta da girma. Ita ja ce, kuma ƙarama. Mutane ba sa son shiga wannan motar.

10

"A shiga! A shiga!" Direba ya daka tsawa. "Yau mun makara sosai," ya gaya masu.

11

Tanko da mahaifiyarsa suka fara shiga. Nan da nan kowa ya shiga cikin jar mota.

12

Tanko ya duba ta taga, sai ya ga mutane da yawa a tashar motar.

13

Mutane da yawa suna gudu don su samu motar. Amma sun makara. Jar motar ta cika. Ta tafi zuwa gari.

14

"Ina babbar shuɗiyar motar?" Mahaifiyar Tanko ta tambaya. "Ta lalace," inji direba. "Ana gyaranta. Za ta zo gobe."

15

Tanko bai damu da launin motar ba. Kuma bai damu da girmanta ba. Wannan motar za ta je gari.

16
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Babbar shuɗiyar mota
Author - Mecelin Kakoro
Translation - Lawali Kaura, Muhammad Tukur Bala
Illustration - Mango Tree
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences