Kai! Wasan Ƙwallo!
Stella Kihweo
Onesmus Kakungi

Ina son mu yi wasa da abokina Chindo.

1

Mun shaƙu sosai da shi, duk inda aka aike ni tare muke zuwa.

2

Wata rana, kakata ta aike ni shago don na sayo mata gishiri da man gyaɗa. Sai na tafi da Chindo.

3

A hanyarmu, sai muka ga abokanmu suna wasan ƙwallo.

4

"Kai! Ka ga ana wasan ƙwallon kafa!" Na ce. Ni ma ina son na yi wasan.

5

Sai na ce wa Chindo, "Mu tambaye su ko za su bar mu mu yi wasan da su. Ina son wasan ƙwallon kafa sosai."

6

Chindo ya ce, "Mu fara zuwa shagon, sai mu dawo mu yi wasan."

7

Sai na ce masa, "Mu fara wasan tukunna!" "Ka san kakata ba za ta bari mu dawo ba."

8

Sai muka haɗu da abokan mu muka yi wasa. Ni ne mai tsaron raga. Ragar an yi ta da manyan duwatsu guda biyu.

9

Na yi ƙoƙari na tsare raga ta, saboda haka, abokaina ba su ci ko ɗaya ba.

10

Mu ka yi ta wasa har sai da fili ya cika da ƙura.

11

Sai muka tafi shago. Ashe kuɗin aiken ya faɗi! Sai na fara kuka. Shi kuma Chindo ya ce da ƙarfi, "Ka daina kuka. Kai ka so a yi wasa tun farko."

12

Mu ka dawo gida ba gishiri kuma ba man gyaɗa. Ga shi duk mun yi duƙun-duƙun cikin damuwa.

13

Muna isa gida, cikin fushi kaka ta ce, "Kuna ina tun-tuni?"

14

Sai ta yafe mana sakamakon faɗar gaskiyar da muka yi. Sannan ta gargaɗe mu ce wa, "Kada mu ƙara zuwa wasa ba da izini ba."

15

Mu ka bai wa agwaginmu abinci, sannan muka wanke jikinmu fes.

16
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Kai! Wasan Ƙwallo!
Author - Stella Kihweo
Translation - Safiya Datti Muhammad, Taiye Fatoki
Illustration - Onesmus Kakungi
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences