Delu Ƙwararriyar 'Yarwasan Kwallon Ƙafa
Eden Daniels
Eden Daniels

Delu ta na kallon yara maza suna wasan ƙwallon ƙafa. Ta so a ce ta na cikin su. Ta tambayi maihorar da 'yanwasan, "Ko za ta iya shiga cikinsu ta yi wasa?"

1

Maihorar da 'yanwasa ya riƙe hannuwansa akan ƙugunsa ya ce, "A wannan makaranta maza ne kaɗai ake bari su yi wasan ƙwallon ƙafa."

2

'Yanmaza suka ce mata ta ta tafi ta yi wasan ƙwallon raga, ita ce ta mata, ƙwallon ƙafa ta maza ce. Delu ta damu.

3

Washe gari, makarantar za ta yi babban wasa. Maihorar da 'yanwasa ya damu saboda ƙwararren Danwasan sa ba ya da lafiya kuma ba zai iya wasa ba.

4

Delu ta ruga wajen maihorar da 'yanwasa ta roƙe shi ya kyale ta, ta yi wasa. Maihorar da 'yanwasa ya rasa yadda zai yi. Sai ya yanke shawra Delu ta shiga cikin su.

5

Wasa ta yi zafi, ba wanda ya ci ƙwallo a farkon rabin lokaci.

6

Lokacin da aka juya rabin lokaci na biyu, sai wani daga cikin su ya turawa Delu ƙwallo. Sai ta ruga da sauri kusa da ƙwallo. Delu ta doki ƙwallo da ƙarfi ta ci.

7

'Yankallo suka miƙe da murna. Tun daga ranar aka ƙyale mata suna yin wasan ƙwallan ƙafa a wannan makaranta.

8
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Delu Ƙwararriyar 'Yarwasan Kwallon Ƙafa
Author - Eden Daniels
Translation - Muhammad Umar
Illustration - Eden Daniels
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs