Saniyar Mu Pendo
Ruth Odondi
Rob Owen

Wannan shi ne Buba.

1

Buba yana son karatun littattafai.

2

Wannan saniyar sunanta Pendo.

3

Pendo tana son cin karas.

4

Buba yana kai Pendo kiwo idan ya dawo daga makaranta.

5

Ya kan shayar da Pendo ruwa a cikin tsabtattaccen kwano.

6

Baba kan zuba wa Pendo hatsi a daro ta ci.

7

Kuma yana tatsar madarar Pendo kullum.

8

Pendo na samar da madara mai tarin yawa.

9

Baba kan kai madarar Pendo shago ya sayar.

10

Buba na jin daɗin shan madara sabuwar tatsa kullum.

11

Cikin murmushi, ya kan dafa ta ya ce, "Na gode, Pendo!"

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Saniyar Mu Pendo
Author - Ruth Odondi
Translation - Philip Hayab John, Suleiman Bello, Timothy Anche
Illustration - Rob Owen
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First words