Tselane Da Ƙato
Lorato Trok
Catherine Groenewald

An yi wata ƙaramar yarinya da ake kira Tselane. Bayan rasuwar ma'aifin, Tselena ta zaman tare da ma'aifiyarta. Wata rana, ma'aifiyarta ta ce mata, za ta ƙaura ta koma wani gari don ta sake wata sabuwar ruyuwa.

1

Tselane ko ba ta son barin garinsu, kuma sai ta yi ta kuka. Ma'aifiyarta ta ji tsoron barin ta ita kaɗai, saboda garin akwai ƙatti da suke ci. Amma Tselane ta yi ta kuka har sai da ma'aifiyar ta yarda ta bar ta.

2

Ma'aifiyar ta ɗauki alkwalin kai ma ɗiyarta abinci kullum. "Zan yi waƙar da za ki gane ni in na zo. Amma kar ki buɗe ma kowa ƙofa," in ji uwar Tselane.

3

Tselane É—iyata! Tselane É—iyata! Fito maza ga abincinki! Fito maza ga abincinki! Tselane É—iyata! Tselane É—iyata! Fito maza ga abincinki! Fito maza ga abincinki!

4

Washe gari, ma'aifiyar Tselane ta zo ta kawo ma ɗiyarta abinci. Ta fara waƙa: Tselane ɗiyata! Fito maza ga abincinki! Tselane ta buɗe ƙofa ta ci abincinta mai daɗi.

5

Ma'aifiyarta ta sumbace ta, kuma ta koma garinta. Tselane ta koma ɗakinta ya kwanta. Ashe wani ƙato yana laɓe bayan wani icce, yana saurare Tselane da ma'aifiyarta!

6

Lokacin da Tselane ta kashe fitila sai ta ji wata babbar murya, na rera waƙar da ma'aifiyarta take bakin ƙofarta. Tselane ɗiyata! Fito maza ga abincinki! "Tafi ka ba ni wuri! Wannan ba ma'aifiyata ba ce," in ji Tselana. "Kai ƙato ne!" ƙato ya tafiyar shi cikin ɓacin rai. Ya koma cikin gidanshi na dutsi.

7

Kullum safe da maraice, ma'aifiyar Tselane tana kawo mata abinci. Kullum safe da maraice, ƙato ya na zuwa shi ma. Amma kullum Tselane na korar shi. Tana gane shi ta babbar muryarshi lokacin da yake kokoyon waƙar.

8

Wata rana, ƙato ya yi tunani ya ce: "Ina iya sauya muryata don ta zama kamar ta ma'aifiyar Tselane." Sai ya fura wuta da yawa kuma saka dutsi masu sulɓi cikin wutar. Bayan dutsin ya yi zafi, sai ya fiddo shi ya hadiye shi! "Gulugulu!" Dutsin ya wuce ta maƙogoron ƙaton.

9

Ƙato ya fara waƙa don ya ji in muryarshi ta sake. Ya yi ta jin daɗi ya ji muryar tashi ta yi kama da ta ma'aifiayar Tselane!

10

Washe gari, ƙato ya je bakin ƙofar Tselana. Ya fara waƙar kamar haka: Tselane ɗiyata! Tselane ɗiyata! Fito maza ga abincinki! Fito maza ga abincinki!

11

Tselani ta ji daɗi da ji muryar ma'aifiyarta. Da buɗe ƙofa, sai ga ƙato! Sai ta so ta rufe ƙofar amma ƙato ya fi ƙarfinta! Ya ɗauki Tselane ya saka ta cikin buhu.

12

Ƙato ya nufi hanyar gidan shi na dutsi, kuma yana waƙar jin daɗi. "In dama ina da kiyar burkutu, da na ji daɗin abincina da dare! Yau sai na ji daɗi!" yake faɗi.

13

Can da hantsi, ma'aifiyar Tselane ta zo ta kawo mata abincin kamar yadda ta saba kullum. Ta rera waƙar, amma Tselane ba ta fito ba. Ta sake rera waƙar, Tselane ba ta amsa ba, shiru! Bayan na ukku, sai ta tura ƙofar. Babu Tselane. Sai ta yi mamakin abin da yake iya faruwa, sai ta yi tunani da gaugawa don samun wata dubara.

14

Sai ta cika wata ƙwarya da giyar burkutu ta ɗaura saman kai, ta tafi wajen gidan ƙato kuma ta sallama mishi. Ƙato da ya ji ƙamshi burkuntun sai buɗe ƙofar ba da ɓata lokaci ba. "Ina wuni ƙato!" in ji ma'aifiyar Tselane. "Ina wucewa na ji kana waƙa da kyau. Yanzu zan je wani garin wajen bikin zagayowar shekarar aifuwar wata ɗiyata."

15

Ƙato ba za bari wannan damar da aka ba shi ta ya sha giyar burkutun! Sai sabkar ma'aifiyar Tselane a gidanshi. "Bari in zuba maka giyar gafin in wuce." In ji ma'aifiyar Tselana. Ƙato yana jin daɗi ya samu giya.

16

Ma'aifiyar Tselane tana zuba mishi yana sha, yana ta sha sai da ya shanye duk ƙwaryar. Yanzu ƙato ya yi tilip! Yana yi maye har barci ya kwashe shi.

17

Lokacin da ma'aifiyar Tselani ta ji ƙato ya fara shinkori, sai ta buɗe buhun suka guda da ita Tselana. Tselana da ma'aifiyarta sun gudu sun koma gida. Tun daga ranar nan, Tselane take tare da ma'aifiyarta cikin sabon garinsu!

18
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Tselane Da Ƙato
Author - Lorato Trok
Translation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid
Illustration - Catherine Groenewald
Language - Hausa (Niger)
Level - Longer paragraphs