Yayyan Biciyoyi: Labaru Wanderimam Danasabe
Nicola Rijsdijk
Maya Marshak

A wani kauye dake ɓangaren Mambilla Plateau a yankin Arewa Maso-Kudu a Nijeriya, in ji wata yarinya mai suna Wanderimam wadda ke taya mahaifiyarta aikin lambu.

1

Wanderimam ta kance yarinyace wadda bata sha'awar zaman gida. Ta yi amfani da wani irin tokobi wajen tona kasa yayin datsa biciyoyi a cikin lambun iyayanta.

2

Wanderimam ta fi sha'war fauɗwar rana kan ko wani lockaci, yayin da ko ina yayi duhu. Lokacin komawarta gida tana bin sakanin shuki da shuki sannan ta haya kogi har ta karaso gida.

3

Wanderimam ta kasance yarinyace mai tsaninin dabara tun kamin shigarta makaranta. Wannan dabaran na ta ya sanya iyayanta suka yanke sha'awara kan su barta a gida ba sai ta yi karatu ba domin ta tayasu aikin gida. Amma daga baya babban yayanta ya sanyanta a makeranta.

4

Ita yarinyace mai son karatu kullum, duk littafin da ta ci karo da shi sai ta ga ta karance shi kaf. wani littafi da ta ci karo da shi. Wannan ya jawo mata nasarar samun yin karatu a Jamiar Ahmadu Bello dake Zaria. Wanderimam ta yi matukar farin ciki domin ita yarinyace mai son sanin abinda duniya ke ciki.

5

A cikin Jamiar Ahmadu Bello dake Zaria, Wanderimam ta kararci sababin abubuwa da dama. Inda take nazarin fannin shuki da rayar da su. Wannen ya tunarta da ita yadde take wasa da yayunta a cikin wani gandu dake Kurmi.

6

Duk wani abun da ta karanta sabo sai ya sanya ta kara son al'umar Jihar Taraba. Burinta a kullum shi ne ta ga suna rayuwa cikin walwala. Duk abun da ta yi nazari, yana sanyata tuna mahaifurta.

7

Bayan kammalawar karatunta, Wanderimam ta dawo Jihar Taraba inda ta tarar komi ya cenza ko kirare na hura wutar babu ga talauci da yunwa ya mamaye ko ina, yara sun dawo Allah Sarki.

8

Nan, Wanderimam ta yi tunanin abunda ya kamata ta yi. Nan ne ta koyawa matan kauyen yadda za su yi datsa biciyoyi da sirrai. Bayan wasu yan lokuta matan sun mori gajiyar abinda suka shuka. Matan sun yi matukar farin ciki kwarai da irin taimako masu da ta yi.

9

Bayan wasu lokata, wanan biciyoyi da suka datsa, ko suka datsa, sun zama gandu harma da samun koramai a cikinta. Wannan abun da Wanderimam ta yi ya bazu a kasa baki ɗaya a yanzu haka sama da biciyoyi miliyan suke raye daga iri na Wanderimam.

10

Daman an ce mai hakuri yaken dafa dutse wataranan ya sha romonta. Duk ko ina a fadin kasan labarinta ya bazu inda ta karba kyaututtuka da dama wanda hakan ya sauyata mace ta farko a cikin kabilar Kuteb da ta karbi lamba ta yabo.

11

Wanderimam ta yi aure a shakara ta 2011. Duk lokacin da muka ga wata biciya mai ban sha'awa, sai mun tuna da ita.

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Yayyan Biciyoyi: Labaru Wanderimam Danasabe
Author - Nicola Rijsdijk
Translation - Ibrahim Yakoko
Illustration - Maya Marshak
Language - Hausa (Nigeria)
Level - Longer paragraphs