Dambu Kashe Mai Zari
Peter Kisakye
Emily Berg

A wani zamani can baya, anyi wani mutum mai Saniya wai shi Alto. Kullun Alto ya kanyi kiwon saniyar. Ya kan kuma shayar da ita. Amma yana amfani da ƙaramar tukunya ne.

1

Don haka sai ya je gidan maƙwabcin sa don ya bashi aron babbar tukunya. Maƙwabcin sa  ya bashi aro ya ce masa, "Ai matsalar maƙwabcin ka taka ce."

2

Bayan wasu yan kwanaki, sai Alto ya je wajen magina tukwane ya sayo wata 'yar qaramar tukunya, ya kai gida. Ya sa ta a cikin babbar tukunyar da aka bashi aro.

3

Bayan ya saka ƙaramar tukunyar a cikin babbar, sai ya ɗora a kan sa. Ya kai gidan maƙwabcin nan da ya bashi aro.

4

Alto ya ce masa, "Na dawo maka da tukunyar da na ara, harma ta haihu." Maƙwabcin ya yi murna da jin cewar tukunyar sa ta haihu. Ya yabi Alto matuƙa harma yayi masa adduar Allah ya yi masa albarka.

5

Bayan kwana biyu, sai Alto ya koma wurin maƙwabcin nan na sa don ya ƙara ara masa babbar tukunyar nan harwayau. Amma fa da mummunar manufa a ran sa.

6

Mai tukunya ya yi ta jira shiru shiru Alto bai dawo da tukunyar ba. A ƙarshe ya je gidan Alto, "Na zo kan batun tukunya ta."

7

Alto ya ce wa maƙwabcin nan nasa, "Ayya abokina, tukunyar nan ta rasu." Yanzunnan nake son zuwa in kai ma baƙin labari.

8

Maƙwabcin nan ya buga tsalle ya yi mamakin wannan al'amari. Cikin fushi ya dakawa Alto tsawa, "Ban taɓa jin inda tukunya ta rasu ba!"

9

Alto ya amsa masa da cewa, "Haba abokina, yakamata ka yarda duk mai haihuwa wata rana zai iya mutuwa. Ni kaina ina jimamin rashin wannan babbar tukunyar."

10

Maƙwabcin ya fusata ya kai ƙarar Alto wurin Alƙali. Da Alƙali ya gama sauraron ƙarar. Sai ya ba maitukunyar rashin gaskiya.

11

"Lokacin da Alto ya zo maka da labarin haihuwar tukunyar ka ai yarda ka yi ba ka yi musu ba. Da ya ce maka duk mai rai inhar zai haihu to zai iya mutuwa, ai haka ne."

12

Maƙwabcin Alto ya koma gida jikin sa a sanyaye tamkar dodonkoɗi. Alto ya mallake babbar tukunyar ta hanyar yaudara.

13
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Dambu Kashe Mai Zari
Author - Peter Kisakye
Translation - Ali Saje
Illustration - Emily Berg
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs