Yarinyar Da Ta Yi Arziki
Salaama Wanale
Mango Tree

An yi wasu ƙannu biyu da ake kira Halima da Fatuma. Uwayensu sun rasu. Ƴan matan biyu suna rayuwa a wani yanki mai hamada. Ba ruwan sama, ba cimaka. Kowa yake son abincin, sai ya yi tafiya mai nisan gaske.

1

Halima yarin ce ma ɗa'a, lafiya da kuma kirki. Ƙanwarta Fatuma tana son rayuwa kuma ba ta jin gargaɗi. Ba ta kula da sauran mutane kuma ba ta darajjanta su.

2

Wata rana, ƙannuwan biyu sun tashi daga barci, kuma sun fiskanci cewa babu abinci ko kaɗan. Sai suka yi niyyar tafiya neman abincin. Halima da Fatuma sun ɗauki hanya dabam-dabam.

3

Lokacin nan, wata tsofuwa da ake kira Amina tana rayuwa kusa da gari. Tana da ƙoƙarin temakawa don tana da arzika. Sai dai Amina tana da kuturta, kuma duk jikinta ƙuraje ne.

4

Fatuma ta haɗu da wannan tsofuyar, da ta kiraye ta "Ɗiyata, kina lafiya? Daga ina kike? Ina za ki?"

5

Fatuma ta amsa duk tambayoyin. Bayan haka, sai tsofuwar matar ta ce, "Maida ni gidana, kuma zan gaya miki abin da za ki yi." Fatuma ta wulaƙanta tsofuyar. Ta ce mata: "Na fi son in mutu da taɓa wannan ƙurajen naki."

6

Tsofuwar ba ta ce komi kuma ta mata fatan ta sabka lafiya.

7

Fatuma ta yi ta tafiya har sai da ta zo wani wuri na mamaki. Wurin akwa shanshani, macizai, kai da duk wani ƙwari. Fatuma ta gaji, kuma ga yunwa saboda ba ta ci komi ba. Ko da ta zamna ta futa, sai ƙwarin suka fito suka cinye ta.

8

Bisan hanyarta, Halima ita ma ta haɗu da tsofuwar. Ta yi farin cikin ganin Amina, saboda ita ce mutum ta farko da ta haɗu da ita cikin wannan bulaguron. Tsofuwar ta kiranyo ta kuma ta muta tambayoyi kamar yadda ta yi ma ƴar uwarta.

9

Fatuma ta yarda ta maida tsofuwar gidanta. "Kin yi aikin da mutane da yawa suka guje ma," in ji tsofuwar. Sai ta ba ma Fatuma wata sanda kuma ta ce mata ta koma gida, can za ta iske duk abin da take so.

10

Fatuma ta gode ma tsofuwar sosai kuma ta yi gaugawa ta koma gida. Ta tarda a gidan, ɗaki cike da kaya da abincin. Ta zamanto it ace ma arzikin garin.

11

Amma ta yi ta kuka da rishin ƙanwarta kuma ta ce, "wandan bai jin gargaɗi zai gamu da mugun abu."

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Yarinyar Da Ta Yi Arziki
Author - Salaama Wanale
Adaptation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid
Illustration - Mango Tree
Language - Hausa (Niger)
Level - Longer paragraphs