Ni Da Iyalina
Waako Joshua
Wiehan de Jager

Da dodona, muna kallon tsuntsaye a sama.

1

Da tsuntsayena, muna ganin baƙin biri cikin icce.

2

Da ni da baƙin birina, muna wasa saman tudu da raƙumman daji.

3

Tare da raƙummana, muna ƙera ƙwallon laka tare da birina.

4

Kullum, tare da birina, muna cin ayaba tare da baƙin biri.

5

Baƙin biri da biri suna tsoron kunkuru.

6

Da kunkuruna, muna komawa gida lafiya da miciji.

7

Da micijina, muna waƙa da bushe-bushe kusan tabki.

8

Iyalina gaba ɗaya muna rayuwa mai daɗi.

9
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Ni Da Iyalina
Author - Waako Joshua, Cornelius Gulere
Adaptation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid
Illustration - Wiehan de Jager
Language - Hausa (Niger)
Level - First sentences