A cikin daji, wata rana lokacin ana yin mugun zafi.
Ƴar Tururuwar ta yi kwanaki da kwanaki ba ta samu ruwan sha ba.
"Ina bukatar ɗashin ruwa ko da wanda ya faɗo ne daga kunnen icce."
Ba bu ko bazara.
"Idan ban sha ruwa ba za ni iya mutuwa," ƴar Tururuwar ta faɗa.
"Ya kamata in tafi tabkin nan, da na ji labarin shi."
"Wanan tabkin yana iya tafiya da ke," wani tsofon Kurege ya yi mata kashedi.
Sai dai wannan ƴar Tururuwar ta ji ƙishirwa ƙwarai.
"Idan ban sha ruwa ba za ni iya mutuwa."
Ƴar Tururuwa ta tafi neman tabkin.
Cikin ciyawa kuma ƙalƙashin reshinen itace busasu.
Har lokacin da ta ji kukan ruwan tabkin.
Ƴar Tururuwa ka ƙwalga sanyayen ruwan tabki.
Tana ta jin daɗi ba ta gani ba ruwan tabki suna bori.
Ƴar Tururuwa ta yi, ta yi ta kama ɗan reshen iccen da yake saman ruwan.
Amma ruwan sun tafi da ita.
"Ku taimake ni. Don Allah ku cece ni."
"Hawo da sauri," in ji Habjiya, da ta riƙe da wani reshen icce ga bakinta.
"Ba za ni tafiya ba har sai na yi ma Habjiyar nan godiya. Za ni jira har lokacin da ta dawo shan ruwa."
Tana cikin jira, wata rana sai ƴan samari biyu riƙe da kaushun harbi suka zo bakin tabkin.
"Akwai wata babar Habjiya da take zuwa wurin ga shan ruwa," ɗaya daga cikin samarin ya faɗa. "Sai mun same ta don mu yi tuwon dare da ita."
"Ba za ni barin ƴan samarin nan ba su kashe wanan Habjiyar ba. Amma kuma ni ƙaramci ya yi mini yawa, to yaya za ni yi?"
A wanan lokacin ne, Habjiyar ta sabko daga saman icce don ta sha ruwa.
Sai ƴar Tururuwar ta samu wata dubara.
Ta hawo saman ɗaya daga cikin samarin, ta cije shi da ƙarfi.
Ɗan sarmayin ya buga tsalo. "Wash!" yana kuwa.
Habjiyar ta ji tsoro kuma ta fira ta koma wani wuri.
Ta haka ne ƴar Tururuwa da gode ma Habjiyar da ta cece ta.