Wani Dogon Mutum
Cornelius Wambi Gulere
Catherine Groenewald

Fartanyar sa yar qarama ce.

1

Kofar dakinsa ma 'yar gajera ce.

2

Gadon barcinsa ma gajere ne.

3

Kekensa ma dan gajere ne.

4

Kai, wannan mutum dogo ne qwarai!

5

Ya maida kotar fartanyarsa mai tsawo sosai.

6

Kyawaren qofofin xakinsa ma ya sanya masu tsayi sosai'

7

Ya maida gadon barcinsa mai tsayi sosai.

8

Ya sayo keke mai tsawo sosai.

9

Ya kan zauna a doguwar kujera. Ya ci abinci da dogon cokali mai yatsu.

10

A qarshe ya bar gidansa, ya koma dokar daji. Ya rayu shekaru masu yawa.

11
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Wani Dogon Mutum
Author - Cornelius Wambi Gulere
Adaptation - Muhammad Tukur Bala
Illustration - Catherine Groenewald
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First words