Delu Qwararriyar 'yar wasar Qwallon qafa
Eden Daniels
Eden Daniels

Delu ta kalli yara maza suna wasar qwallon qafa. Ta yi shaawar shiga tayi wasar da su. Ta tambayi Maihorar da 'yan wasar, "Ko zata  iya shiga ayi wasar da ita?"

1

Maihorar da 'yan wasar ya riqe qugunsa da hannuwansa. "A wannan makarantar, Maza ne kawai aka yarda suyi wasan qwallon qafa." Ya ce.

2

'Yan mazan suka ce mata, "Ta je tayi wasan qwallon raga." Suka ce, "Qwallon raga na mata ne, qwallon qafa kuwa na maza ne." Wannan ya vata wa Delu rai.

3

Washe gari, makarantar tana da babban wasa. Maihorar da 'yan wasan ya damu matuqa saboda haziqin xanwasan sa bashi da lafiya, bazai sami dammar yin wasa ba.

4

Delu ta roqi Maihorar da 'yan wasa cewa, "Don Allah ka bani dama in buga wasan." Maihorarwar, ya rasa abin da zaiyi. Sai ya yanke shawarar sa Delu cikin 'yan wasan.

5

Wasa ya yi zafi. Duk qungiyoyin basu sa qwallo a raga ba har zuwa hutun rabin lokaci.

6

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Delu ta amshi qwallo. Sai ta ja qwallon zuwa ragar abokan karawar su. Sai Delu ta daki qwllon da karfi sai ta shiga raga.

7

Taron 'yan kallo sunyi ihu don murna. Tun dag wannan lokaci, aka baiwa 'Yan mata damar yin wasan qwallon qafa a makarantar.

8
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Delu Qwararriyar 'yar wasar Qwallon qafa
Author - Eden Daniels
Translation - Habibu Ahmed Jibrin
Illustration - Eden Daniels
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs