Mitsitsin Iri: Labarin Wangari Maathai
Nicola Rijsdijk
Maya Marshak

A ƙasar Kenya, a cikin wani ƙauye mai tsaunuka da kwazazzabai, an yi wata yarinya mai taya mahaifiyarta aiki a gona. Sunan yarinyar Wangari.

1

Wangari na sha'awar zama a waje, shi ya sa ta shuka iri a lambun gidansu.

2

Lokacin da tafi son tafiya gida shi ne bayan faɗuwar rana. Ta na bin kwararo don zuwa gida da kuma kallon shuke-shuke.

3

Wangari yarinya ce mai ƙwazo da son zuwa makaranta. Amma iyayenta sun fi son ta taya su aikin gida. Da ta cika shekara bakwai sai yayanta ya rinjayi iyayenta domin ta je makaranta.

4

Wangari ta yi murna matuƙa lokacin da aka gayya ce ta zuwa Amurka ta yi karatu, sakamakon ƙwazonta na son karatun littattafai.

5

A Jami'ar Amuruka ta koyi sababbin abubuwa da yawa. Waɗanda suka haɗa da rayuwar tsirrai da yadda suke girma. Sannan, da yadda suke wasa da 'yan uwanta a ƙarƙashin inuwar kyawawan bishiyoyin Kenya a daji.

6

Da zarar ta koyi wani abu ya kan ƙara mata ƙaunar mutanen Kenya, tana son ganin su cikin farin ciki da 'yanci. Sannan, takan tuna Afirika a matsayin gida.

7

Yayin da ta kammala karatunta, sai ta dawo gida. Amma, ƙasarta ta sauya. An sami manyan gonaki a ƙasar. Mata ba su da itacen girki sannan, jama'ar gari sun talauce, kuma yara suna fama da yunwa.

8

Wangari tayi tunanin abun yi. Ta koyawa mata dabarun shuka irin itatuwa. Mata na sayar da itatuwa da amfani da kuɗin domin kula da iyali. Matan sun kasance cikin farin-ciki. Wangari ta taimaka sun zama masu ƙwazo da matsayi.

9

Bayan lokaci mai tsawo bishiyoyin sun girma aka fara samu gandun daji. Koguna suka fara gudana, saƙonta ya fara mamaye Afirika. A yau miliyoyin bishiyoyi sun samu a sakamakon gudunmuwar irin da Wangari ta samar.

10

Mutanen duniya baki ɗaya sun yaba da ƙwazon Wangari. Saboda haka ne, aka karrama ta da shahararriyar kyautar nan ta zaman lafiya ta duniya (NOVEL). Ita ce mace ta farko da ta fara samun kyautar a Afirika.

11

Wangari ta rassu a shekara ta dubu biyu da sha ɗaya (2011), amma mukan tuna ta duk lokacin da muka ga kyawawan bishiyoyi.

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Mitsitsin Iri: Labarin Wangari Maathai
Author - Nicola Rijsdijk
Translation - Rabi'u Aminu Lawan, Taiye Fatoki
Illustration - Maya Marshak
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs