Giwa guda ɗaya ta nufi wajen shan ruwa.
Raƙuman dawa guda biyu, suna tafiya shan ruwa bakin tafki.
Bakane guda uku da tsuntsaye huɗu su ma suna tafiya shan ruwa.
Barewa biyar da wasu Gwankaye guda shida na tafiya tafki shan ruwa.
Jakunan daji guda bakwai na gudu zuwa tafki don shan ruwa.
Kwaɗi guda takwas da kifaye tara na yin ninƙaya a cikin tafki.
Wani zaki ya yi gurnani. Shi ma yana son shan ruwa. Waye ba ya tsoron zaki?
Wata giwa bata jin tsoron zaki domin tana shan ruwa tare da zakin.